Banagaren kasa da kasa: Rahman Khan mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Indiya ya bada labarin cewa: kasarsa za yi amfani da tsarin tattalin arziki irin na Musulunci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta FT>CON ta bayyana cewa: Rahman Khan mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Indiya ya bada labarin cewa: kasarsa za yi amfani da tsarin tattalin arziki irin na Musulunci. Da dama daga cikin kasashen duniya da na musulmi da wadanda ban a musulmi ba a turai da asiya da Afrika sun fara bayyana alhininsu na amfani da tsarin tattalin arziki irin na Musulunci kuma wannan bukata ta fara yawaita net un bayan da tattalin arzikin Amerika da na Turai suka fuskanci matsalar da cikas mai karfi.
532001