Bangaren kasa da kasa:Wani bangare na musulmi da wadanda ba musulmi ba a Indiya a wani matakin fahimtar juna da bayyana fuskar Musulunci sun fara yada bincike kan addinin Musulunci da Ma'aikin Allah (SWA).
Bayan ta nakalto daga jaridar Alnadwa da ake bugawa a kasar Saudiya cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Wani bangare na musulmi da wadanda ba musulmi ba a Indiya a wani matakin fahimtar juna da bayyana fuskar Musulunci sun fara yada bincike kan addinin Musulunci da Ma'aikin Allah (SWA). Wannan kokari ya samu karbuwa da jinjinawa daga kungiyoyi daban daban na musulmi da wadanda ba na musulmi ba a wannan kasa da kuma yadda hakan zai kara kusanci a tsakanin al'ummar wannan kasa da rayuwarsu ta zamantakewa.
540815