Bangaren al'adu da fasaha; malamai ashiri ne daga cikin malaman akadaimiyar ulumin Islami a Afaganistan suka ziyarci Darul Hadis.
Daga Afganistan ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: malamai ashiri ne daga cikin malaman akadaimiyar ulumin Islami a Afaganistan suka ziyarci Darul Hadis. Malaman sun ziyarci gurare daban-daban da suka hada da bangaren fikhu,dokoki,tafsiri,hadisi akida da ala'du har ila yau kuma an yi masu bayani dalla-dalla kan irin ayyukan da wannan darul Hadisi ke aiwatarwa a wannan kasa ta Afganistan. A wannan ganawa Muhammad Muradi shugaban bangaren tarjuma a wannan muassisa bayan godiya ga tawagar malaman ya kuma yi bayani kan irin ayyukan da suke gudanarwa filla-filla.
542502