IQNA

Bincike Kan Dangantakar Al'adu Tsakanin Iran Da Indiya

Bangaren al'adu da fasaha; banagaren hulda da al'adu na jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma na Indiya a wani zama sun fara bincike kan dangantakar kasashen biyu.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; banagaren hulda da al'adu na jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma na Indiya a wani zama sun fara bincike kan dangantakar kasashen biyu. Ali Muhammadi karamin ofishin jakadancin Iran a cikin wani jawabin day a gabatar a lokacin wannan zama ta kara hulda da juna ta fuskar yare da adabi na farisanci a jami'ar Islamil Yusuf da kuma wasu jami'ai da suka halarta sun gabatar da jawabai masu gamsarwa da kuma hanyoyin da za a bi wajen cimma burin da ake son cimmawa.

542407