IQNA

Zimbabwe Za Ta Dauki Nauyin Taron Kara Sanin Sirar Ma'aikin Allah (SWA)

Bangaren tunani da ilimi: kasar Zimbabwe ta dauki nauyin gudanar da taron sanin sirar ma'aikin Allah .
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: kasar Zimbabwe ta dauki nauyin gudanar da taron sanin sirar ma'aikin Allah . Wannan taro na Zimbabwe ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar Musulunci a Iran ya shirya wannan taro na Zimbabwe tare da hadin guiwar yan jami'a musulmi a jami'ar wannan kasa da kuma za a samu halartar yan jami'a da malaman jami'ar musulminsu da kiristocinsu.Burin wannan taro shin karawa juna sani kan tarihin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidan da kuma bayyanawa wadanda ba musulmi ba wane ne Hadarat Muhammad tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa .

542857