IQNA

Kiristocin Jodan Sun Ce Mamaye Masallacin Ibrahima Wani Ta'adancin Wariya ne

Bangaren siyasa da zamantakewa' hadin guiwar kiristocin Jodan sun ce suna daukan duk wani mataki na mamaye da mallakar masallacin annabi Ibrahima(AS) da kabarin Bilal a matsayin wani ta'addanci da wariyar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila kan musulmin Palasdinu.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta na kasar Jodan ta watsa rahoton cewa; zamantakewa' hadin guiwar kiristocin Jodan sun ce suna daukan duk wani mataki na mamaye da mallakar masallacin annabi Ibrahima(AS) da kabarin Bilal a matsayin wani ta'addanci da wariyar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila kan musulmin Palasdinu. Kuma za su bi duk wata hanya da salo wajen yakar wannan mummunan mataki da Haramtacciyar kasar Isra'ila ke kokarin dauka. Kuma tuni kungiyoyi daban-daban da suka hada da na kare hakkin dan adam da na addinai suka fara tofa tofin Allah tsine kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da wannan mataki na tsangwalar fada da ta bullo da shi.

543645