Bangaren al'adu da fasaha: a karon farko za a fara taro kan saka hannayen jari na musulmi a gabas ta tsakiya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga reshenta daga kasar Jodan bayan ta nakalto daga jaridar Alwasat ta kasar Bahrain ta watsa rahoton cewa; a karon farko za a fara taro kan saka hannayen jari na musulmi a gabas ta tsakiya. A wannan taro mahalarta taron za su yi bayani dalla-dalla kan muhimmanci saka hannayen jari a tsakanin kasashen musulmi da kuma muhimmancin haka a gabas ta tsakiya da irin moriyar abin da za a cimma da alfanon da ke tattare da hakan.
546596