IQNA

Taron Kasashen Duniya Kan Ganin Wata A Malaishiya

Bangaren kasa da kasa; a kasar Malaishiya ne za a gudanar da taron kasashen duniya dangane da ganin wata.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Koweiti Kuna ta watsa labarin cewa; wata gagaramar tawaga da ta hada muassishishi da sakatarorin hadin guiwar kungiyoyin ganin wata na duniya za su gudanar da wannan taro kan yadda za a magance matsalar ganin wata kuma za a samu halartar masana ilimi kan harkokin tattalin arziki da addini da lamura na zaman takewa a kasashen musulmi da wadanda ban a musulmi ba.Kuma burin gudanar da wannan taro shi ne gudanar da bincike da samar da wata hanya mai inganci da kowa zai amince da ita kan hanyoyin ganin wata.

550468