Bangaren siyasa da zamantakewa;ministan harkokin waje na kasar Suriya a jiya ne ya bukaci kasashen duniya da su matsa lamba kan yahudawan sahayoniya na su kawo karshen killacewar da suka yi yankin zirin gaza.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga reshenta na kasar Suriya ta watsa rahoton cewa; ministan harkokin waje na kasar Suriya a jiya ne ya bukaci kasashen duniya da su matsa lamba kan yahudawan sahayoniya na su kawo karshen killacewar da suka yi yankin zirin gaza.Har ila yau ministan ya kawo bayani dalla-dalla kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma irin zaluncin da take aikatawa na wuce gonad a irin da cin zalin da take nunawa al'ummar Palasdinu musamman palsdinawan da ke zaune a yankin Zirin Gaza.
550553