IQNA

A Katar An Bude Kasuwar Baje Koli Ta Kasa Da Kasa Kan Fasaha

Bangaren kasa da kasa ;a kasar Katar Ne aka bude kasuwar baje koli ta kasa da kasa kan rubutun larabci da fasaha a Musulunci da aka bawa sunan Aklam.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur;ani a Iran ikna ce bayan ta nakalto daga jaridar kasar ta Katar Alshark ta watsa labarin da ke cewa; a birnin Doha fadar mulkin kasar Katar Ne aka bude kasuwar baje koli ta kasa da kasa kan rubutun larabci da fasaha a Musulunci da aka bawa sunan Aklam.A lokacin bude wannan kasuwar baje kolin an samu halartar babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ikmalul Dine Ihsan Uglan da kuma Ahmad bin Abadallah Almari ministan da ke kula da harkokin addini a wannan kasa ta Katar da kuma jakadu masu yawa da ke zaune a wannan kasa.


551652