IQNA

A Suriya Ne Za A Gudanar Da Taro Kan Kusanci A Tsakanin Mazhabobi

Bangaren tunani da nazari:a kasar Suriya ne za a gudanar da taro kan kusanci tsakanin mazhabobi karo na shidda inda za a samu halartar Ayatullahi Taskhiri babban sakataren kungiyar kusanci a tsakanin mazhabobi.
Cibiyar da ke kula da harkokin harkokin kur'ani a Iran Ikna daga reshenta na hukumar da ke kula da yada al'adun Iran da dangantaka ta Musulunci ta watsa rahoton cewa; a kasar Suriya ne za a gudanar da taro kan kusanci tsakanin mazhabobi karo na shidda inda za a samu halartar Ayatullahi Taskhiri babban sakataren kungiyar kusanci a tsakanin mazhabobi. Wannan wani babban mataki ne da zai kara habaka dangantaka a tsakanin kasashn musulumi da musulmi a fadin duniya musamman idan aka yi la'akari da yadda dangantaka ta kud da kud da ake da kwai a tsakanin musulmi da mazhabobi na duniya. Kuma ofishin da ke kula da yada al'adu na jamhuriyar Musulunci a ketare n eke kula da tuntubar juna kan wannan taro.


552853