IQNA

A Suriya Za A Gudanar Da Taro Kan Mu'ujizar Ilimi Da Ke Cikin Kur'ani

Bangaren harkokin kur'ani;ministan harkokin addini Musulunci a Suriya ya bada labarin gudanar da taro kan sanin mu'ujizar ilimi da ke cikin Kur'ani mai girma kuma za a gudanar da wannan taron bincike a watan mai kamawa a wannan kasa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga reshenta da ke kasar Suriya bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin Musulunci a wannan kasa ta watsa rahoton cewa; ministan harkokin addini Musulunci a Suriya ya bada labarin gudanar da taro kan sanin mu'ujizar ilimi da ke cikin Kur'ani mai girma kuma za a gudanar da wannan taron bincike a watan mai kamawa a wannan kasa. Minista Muhammad Abdul Sattar Alsaid a wata ganawa ce day a yi da wani gungun malaman masallatai a lardin gabacin Suriya ya bayyana cewa; a watan gobe ne ma'aikatarsa za ta gudanar da taro kan binciken irin mu'ujizar ilimi da ke cikin kur'ani.

557975