Bangaren nazari; za a gudanar da taron kasa da kasa na Alama Kashiful Gida'a inda za a samu halartar manyan masana malamai na ilimi a duniyar muslmi da za su halarta kuma a cikin shekaru biyu masu zuwa sau biyu ne za a gudanar da wannan taro.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga babban ofishi da ke hulda da jama'a da kuma bangaren hulda ta kasa da kasa a ofishin yada addinin Musulunci a hauza ta ilimi ta birnin Qum ya watsa rahoton cewa; za a gudanar da taron kasa da kasa na Alama Kashiful Gida'a inda za a samu halartar manyan masana malamai na ilimi a duniyar muslmi da za su halarta kuma a cikin shekaru biyu masu zuwa sau biyu ne za a gudanar da wannan taro. Hujjatul Islama Walmuslim Ahmad Mubalig ya bayyana cewa : wannan taro zai yi nazari ne matsayi da ayyukan da wannan bawon Allah ya gudanar a lokacin rayuwarsa da kuma rawar day a taka wajen yada ilimi da addini.
557956