IQNA

Taro Kan Sulhu Na Gaskiya Da Adalci Da Tattaunawa Ta bai Daya A Indiya

Bangaren ilimi da nazari: a kasar Indiya ne za a gudanar da taron kan tabbatar da sulhu na gaskiya da tattaunawa ta bai daya a fadin duniya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta da ke hukumar da ke kula da yada al'adun Iran a ketare da kusanci a tsakanin kasashen musulmi ta watsa rahoton cewa; a kasar Indiya ne za a gudanar da taron kan tabbatar da sulhu na gaskiya da tattaunawa ta bai daya a fadin duniya. A wajen wannan taro masana da manazarta da suka shafi al'adu za su yi nnazari da bincike kan hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da sulhu na gaskiya da adalci ta hanyar tuntuba da tattaunawa ta bai daya da kuma masanan za su fito daga kasashen Japon,Filipine.Serilanka,Malaishiya,Indonosiya,Tailand,Indiya Da Snagapur.


558300