IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Adabin Farisanci Da Larabci A Labanon

Bangaren al'adu da fasaha: bisa la'akari da dangantaka ta kud da kud tsakanin al'adun farisanci da larabci da kuma matsayinsu ne aka shirya taron kasa da kasa a kasa Labanon da zai yi nazari kan abubuwan da suka hada su.
Daga reshenta da ke hukumar da ke kula da yada al'adun kasar Iran a ketare cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; bisa la'akari da dangantaka ta kud da kud tsakanin al'adun farisanci da larabci da kuma matsayinsu ne aka shirya taron kasa da kasa a kasa Labanon da zai yi nazari kan abubuwan da suka hada su.
Kuma malaman yarukan biyu da adabin Farisanci da larabci talatin ne da kasashen Iran ,Labanon ,Suriya,Jodan ,Masar ,Maroko,Tunusiya,Faransa da Afganistan za su gabatar da jawabi a gurin wannan taro.

558861