IQNA

Lardin Ujlan Na Jodan An Kafa Masa Bankin Musulunci

Bangaren al'adu da fasaha:an kafa sabon reshen bankin Musulunci na kasa da kasa a lardin Ujlan na kasar Jodan.
Bayan ta nakalto daga jaridar Alrayi da ke fitowa a kasar Jodan ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; an kafa sabon reshen bankin Musulunci na kasa da kasa a lardin Ujlan na kasar Jodan.An gudanar da bukin bude wannan sabon bankin Musulunci ne tare da halartar manyan jami'an gwamnatin lardi da wakilin gwmnaan yankin da mutanan gari da suka nuna farin cikinsu kan wannan banki da irin alfanon da ke tattare da wannan banki.



558734