IQNA

Kungiyar Masana Matasa A Suriya Za Su Kare Palasdinawa

Bangaren al'adu da fasaha: hadin guiwa da kungiyoyin masana matasa a kasar Suriya suna nan suna kimtsa yadda za su shigar da karar haramtacciyar kasar Isra'ila kan yadda take zaluntar al'ummar Palsdinu da tilasta masu yin gudun hijira daga yankin yammacin kogin jodan.
Daga reshenta da ke kasar Suriya bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai na gwamnatin kasar ta Suriya Sana,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; hadin guiwa da kungiyoyin masana matasa a kasar Suriya suna nan suna kimtsa yadda za su shigar da karar haramtacciyar kasar Isra'ila kan yadda take zaluntar al'ummar Palsdinu da tilasta masu yin gudun hijira daga yankin yammacin kogin jodan.Wannan hadin guiwa mai sunan Jini a kan Hanya na bayanin yadda ake zubar da jinin bayun Allah fararen hula yan Palsdinu a fadin yankunan su ba take da an nuna masu tausayi ko jin kai ba ko kuma wata kungiyar ta kasa da kasa t ace uffin kan wannan lamari.


564326