Bangaren kasa da kasa;an fara gasar hardar Hadisi na ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa karo na sha hudu a hadediyar daular larabawa a kyautar da ake yi wa lakabi ta kyautar Sharja da aka fara a ranar sha daya ga watan ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar Al'ittihad da ke fitowa a hadeddiyar daular larabawa ta watsa rahoton cewa; an fara gasar hardar Hadisi na ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa karo na sha hudu a hadediyar daular larabawa a kyautar da ake yi wa lakabi ta kyautar Sharja da aka fara a ranar sha daya ga watan ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara. Kuma wannan gasar mu'assisar kula da harkokin kur'ani mai girma da sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare ta Sharja.
571198