IQNA

Taron Fahimtar Juna Na Musulmi a Atlanta

Bangaren kasa da kasa: muslmin Atlanta za su gudanar da taro a tsakaninsu da zummar hada kan al'ummar musulmin Amerika a karkashin tuta guda ta Musulunci daga ranar ashirin da biyar zuwa ashirin da bakwai na watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta webstarts .2 ta watsa rahoton cewa; : muslmin Atlanta za su gudanar da taro a tsakaninsu da zummar hada kan al'ummar musulmin Amerika a karkashin tuta guda ta Musulunci daga ranar ashirin da biyar zuwa ashirin da bakwai na watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.A wajen wannan ganawa za a yi magana kan rawar da mata musulmi ke takawa,abubuwan ci gaba na addinin Musulunci, bada horo na Musulunci, Manzonnin Da Allah ya aiki su,fahimtar kalmar Jalala Ta Allahu suna daga cikin abubuwan da za ayi magana a kansu a wajen taron da jawabai kansu.




578196