IQNA

Za A Bawa ladannai Horo A Turkiya

Bangaren kasa da kasa; ofishin da ke kula da masu bayar da fatawa a birnin Istambul na kasar Turkiya na da niyar koyar da ladannai yadda ake kiran Sallah a wannan gari.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto daga internethaber ta watsa rahoton cewa; ofishin da ke kula da masu bayar da fatawa a birnin Istambul na kasar Turkiya na da niyar koyar da ladannai yadda ake kiran Sallah a wannan gari. Mustapha Cagar'iji mai bada fatawa a birnin Istambul ya fitar da bayani da ke cewa; kimanin masallatai dubu uku n eke akwai a wannan birni saboda haka bada horo ga ladannai zai taimaka matuka gaya ko shakka babu.


579395