IQNA

Za A Sanya Koyar Da Rayuwar Ma'aiki A Makarantun Rasha

Bangaren kasa da kasa: Littafin da ya kumshi takaitaccen bayani kan rayuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi za a fara koyar da shi a cikin jerin manhajar koyar da darasi a kasar Rashha da kuma ya kumshi bangaren ilimi,tarihi da ruwayoyin hadisai da kuma bangaren bincike na masana na karnonin da suka gabata da wannan karni da muke ciki.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna ta watsa rahoton cewa; Littafin da ya kumshi takaitaccen bayani kan rayuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi za a fara koyar da shi a cikin jerin manhajar koyar da darasi a kasar Rashha da kuma ya kumshi bangaren ilimi,tarihi da ruwayoyin hadisai da kuma bangaren bincike na masana na karnonin da suka gabata da wannan karni da muke ciki.Wannan mataki nada matukar muhimmanci matuka gaya musamman idan aka yi la'akari da wannan kasa ta Rasha da kum ayanayin da musulmi ke rayuwa a cikinta da kuma yadda yayansu ke daukan darasi a makarantun.





588182