IQNA

Masu Harkokin Addini A Tajikistan Sun Ziyarci Karamar jami'ar Mashhad

Bangaren kasa da kasa 'malamai da masu bincike kan harkokin addini a kasar Tajikistan sun ziyarci karamar jami'a da ke koyar da ilimin sanin Allah a jami'ar birnin Mashhad.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga yankin Khurasan Radawi ta watsa rahoton cewa; 'malamai da masu bincike kan harkokin addini a kasar Tajikistan sun ziyarci karamar jami'a da ke koyar da ilimin sanin Allah a jami'ar birnin Mashhad. Wannan tawaga da ke karkashin limamin juma'a na birnin Wahadat na kasar Tajikistan ta ziyarci birnin na Mashhad ne a ranar ashirin ga watan Khurdad na shekarar hijira shamsiya dubu daya da dari uku da tamanin da tara kuma wannan tawaga ta gana da tattaunawa da shugaba da mukaddashai da shugabannin bangarori na koyarwa a karamar jami'ar.


595476