IQNA

Ihsan Uglo Za A Bashi Digirin Girmamawa Na Uku

Bangaren kasa da kasa; Ikmalul Din Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin da biyar ga watan Khurdad wato jiya ke nan ya karbi digirin girmamawa na uku da jami'ar Musulunci ta Malaishiya tab a shi.

Cibiyar da ke kula da harkokin da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga gercekgundem ta watsa cewa : Ikmalul Din Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin da biyar ga watan Khurdad wato jiya ke nan ya karbi digirin girmamawa na uku da jami'ar Musulunci ta Malaishiya tab a shi. Ihsan Uglo a daidai lokacin day a ke ziyarar ganawa da jami'an gwamnati da na addini a kasar Malaishiya a jiya jami'ar Musulunci ta malaishiya ta girmama shi ta hanyar ba shi digirin girmamawa na uku tare da jinjina masa kan jan aiki masu muhimmanci day a ke gudanarwa karkashin wannan kungiya da ta hada kasashen musulmi a fadin duniya da kokarin hada kan kasashen musulmi.


597664