IQNA

Kwamitin Jami'oin Musulunci Za fara Zamansa A Birnin Damascus

Bangaren fikira da ilimi; Kwamitin jami'oin Musulunci zai fara gudanar da zamansa a birinin Damascus fadar mulkin kasar Syria, tare da halartar masana daga sassan duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na Muhit an bayyana cewa, kwamitin jami'oin Musulunci zai fara gudanar da zamansa a birinin Damascus fadar mulkin kasar Syria, tare da halartar masana daga sassan duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai mayar da hankali ne kan batutuwa da suka shafi harkokin kiwon lafiya da kuma ilimi mai zurfi a kasashen musulmi.598169