Bangaren al'adu da fasaha; shugaban cibiyar tarjama da yada abubuwan ilimi na Musulunci ta bada labarin tarjama Sahifar Sajjadiya a cikin yaruka hudu na duniya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta da ke hukumar yada al'adun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ketare da kuma kara kusanci a tsakanin kasashen musulmi da musulmin duniya ta watsa rahoton cewa; shugaban cibiyar tarjama da yada abubuwan ilimi na Musulunci ta bada labarin tarjama Sahifar Sajjadiya a cikin yaruka hudu na duniya.Hujjatul Islam Walmuslim Asgar Sabari shugaban cibiyar samadahi da tarjama da watsa abubuwan addini ne ya bada wannan labari na tarjama sahifa sajjadiya a cikin yarukan Istambuli,Azari,Japoni Da Spaniyanci.
601490