Bangaren al'adu da fasaha; An buga wata sabuwar nashriyya da shafi canje-canjen da ake samu a bangarorin al'adu wanda karamin ofishin jakadancin Iran a Doha ya buga.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, reshen bangaren bunkasa al'adu na kasar Iran a birnin Doha na kasar Katar ya habarta cewa, an buga wata sabuwar nashriyya da shafi canje-canjen da ake samu a bangarori daban-daban na al'adu wanda karamin ofishin jakadancin Iran a Doha ya buga. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin wannan nashriyya an kawo muhimman batutuwa da suka danganci harkoki na al'adu da suke da dangantaka da Musulunci kai tsaye, kamar ayyukan da ake gudanarwa a masallatai, da raya tarukan addini. A bangare guda kuma ta tabo wasu batutuwa na siyasa, kamar zanga-zangar Azhar da ke yin Allawadai da killace zirin Gaza.603422