IQNA

An Fassara Kundin Tsarin Mulkin Iran A Cikin Harshen Karkizi

Bangaren al'adu da fasaha: a karon farko ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Karkizistan sun tarjama kundin tsarin mulkin jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yaren Karkizi.

Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshen hukumar da ke kula da al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma kusanci a tsakanin kasashen musulmi da musulmi a duniyar musulmi ta watsa rahoton cewa; a karon farko ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Karkizistan sun tarjama kundin tsarin mulkin jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yaren Karkizi. Muhammad Husein Abidini ma kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar Ta Karkizistan a lokacin bukin bayyana muhimmancin yaren farisanci da kuma muhimmancin tarjama wannan kundi na tsarin mulki na jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bada wannan labarin da burin kaddamar da wannan aiki.





603289