Bangaren fikira da ilimi; An gudanar da wani zaman taro a birnin Moscow na kasar Rasha, wanda ya yi dubi kan hanyoyin karfafa danganta tsakanin Rasha da kuma kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren yada al'adu na da bunkasa harkokin ilmi da ke birnin Moscow an habarta, an gudanar da wani zaman taro a birnin Moscow na kasar Rasha, wanda ya yi dubi kan hanyoyin karfafa danganta tsakanin Rasha da kuma kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya mayar da hankali kan yadda za a kara bunkasa dangantaka tasakanin bangarorin biyu, tare da tabo batun rikicin palastinawa da haramtacciyar kasar Is'ila.604882