Bangaren al'adu da fasaha; A kowace shekara a daidai wannan lokaci cibiyoyin musulmi a sassa daban-daban na kasar Amurka suna gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi (AS) domin raya wannan raa mai albarka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A kowace shekara a daidai wannan lokaci cibiyoyin musulmi a sassa daban-daban na kasar Amurka suna gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi (AS) domin raya wannan ran mai albarka ga dukkanin al'ummar musulmi na duniya.
Taron na tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imamul hujja (AS) taro da wasu bangarori dab a musulmi ba suke kallonsa a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci a wurinsu, bisaa'akari da cewa batun bayyanar wani mutum a karshen duniya domin ceto al'umma daga duhun halaka da danniya da zalunci, wani abu ne wanda akasarin mabiya addinai na duniya sun yi imani da shi.
Taron yak an samu halartar musulmi mabiya mazhabar shi'a da 'yan sunna da kiristoci, har ma da yahudawa wadanda bas u yi iamni da akidar sahyuniyanci ba.
621824