Bangaren fasaha, Za a gudanar da zaman taron babbar gamayar radiyo da talabijin ta kasa a cikin makon gobe, wanda zai samu halartar wakilai daga sassa daban-daban na kasa da kuma kasashen ketare.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, za a gudanar da zaman taron babbar gamayar radiyo da talabijin ta kasa a cikin makon gobe, wanda zai samu halartar wakilai daga sassa daban-daban na kasa da kuma kasashen duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taron zai mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa da suka dangaci sadarwa a kasashen musulmi, da kuma abin da ya kamata kafofin sadarwa na kasashen musulmi su mayar da hankali kansu.
Yanzu haka dai mambobin wannan gamayya sun kammala dukkanin shirye-shiryensu na gudanar da wannan zaman taro, gamayyar na da mambobi 195 da suka fito daga kashe 29 na duniya.
667035