IQNA

Sama Da Kayayyakin Sadarwa 380 Aka Nuna Taron Sadarwar Kasashen Musulmi

Bangaren kasa da kasa, Sama kayayyakin sadarwa 380 ne aka kawo a wajen taron kafofin sadarwar kasashen musulmi da aka gudanar a birnin Tehran, wanda ya samu halartar gidajen talabijin da radiyo.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na taroon gidajen radiyo da talabijin cewa sama kayayyakin sadarwa 380 ne aka kawo a wajen taron kafofin sadarwar kasashen musulmi da aka gudanar a birnin Tehran, wanda ya samu halartar gidajen talabijin da radiyo.

Bayanin ya kara da cewa wannan taro yana daya daga cikin muhimman tarukan sadarwa da ake gudanarwa a shekara a birnin Tehran tare da wakiltar wakilan cibiyoyi.

Yanzu haka dai an bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo a wannan zaman taro da aka gudanar a matsayi na kasa da kasa a birnin Tehran.

673961