Bangaren kasa da kasa; taro kan tafsirin suratul Naml da za a gudanar a ranar sha biyar ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a jami'ar yin nazarin kur;ani ta Britaniya da ke birnin Landon.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta iidr ya watsa rahoton cewa: taro kan tafsirin suratul Naml da za a gudanar a ranar sha biyar ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a jami'ar yin nazarin kur;ani ta Britaniya da ke birnin Landon. Shi dai wannan taro na kwana daya ne da za a fara da misalin karfe tara agogon London har zuwa karfe shida da rabi na marece kuma za a yi nazari ta bangarori daban daban na Suratul Naml.
678169