Bangaren kasa da kasa; hukumar kula da ilimi da al'adun Musulunci ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi Asesko ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da harin da aka kai wa wata coci a birnin Bagadaza inda harin ta'addancin kan wannan coci ya yi sanadiyar kisan Saida Alnajatu.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiya ta kusa da Isesko ya watsa rahoton cewa; hukumar kula da ilimi da al'adun Musulunci ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi Asesko ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da harin da aka kai wa wata coci a birnin Bagadaza inda harin ta'addancin kan wannan coci ya yi sanadiyar kisan Saida Alnajatu. Wannan hari wani sabon makirci da zagon kasa ne na kokarin haddasa kirici da fitina a tsakanin musulmi da kiristoci a kasar ta iraki da hakan ya yadu a sauran kasashen musulmi a daidai wannan lokaci na halin dardar da ake ciki.
687852