IQNA

Limamin Juma'ar Najaf Ya Jaddada Ziyartar Haramin Imam Huseini (AS) Ranar Arafat

Bangaren kasa da kasa :Said Sadrul din Kabanci limamin juma'a na birnin Najaf Ashraf ya jaddada muhimmancin ranar Arafat da yin ziyartar hubbarin Aba Abdullahi Alhuseini (AS) a wannan rana.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiya ta kusa da Kafanci ya watsa rahoton cewa; Said Sadrul din Kabanci limamin juma'a na birnin Najaf Ashraf ya jaddada muhimmancin ranar Arafat da yin ziyartar hubbarin Aba Abdullahi Alhuseini (AS) a wannan rana. Shi dai limamin juma'ar birnin Najaf din ya yi bayani dalla-dalla kan abubuwan day a kamata mutane su maida hankali wajen ziyartar wannan Hubbarin da kuma a wannan rana ta Arafat kuma ya fadi haka ne a ranar ashirin da daya ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya kuma ya gabatar da wannan hudubar sallar juma'ar ce a Huseiniyar Fatimiya da ke birnin Najaf mai tsarki.


694288