Bangaren kasa da kasa' birnin Koforida na kasar Ghana za a kaddamar da makarantar ilimin addinin Musulunci ta koloji a kokarin da ake yin a ganin an kara bunkasa harkokin ilimi a wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Ghana Web ya watsa rahoton cewa; kasa' birnin Koforida na kasar Ghana za a kaddamar da makarantar ilimin addinin Musulunci ta koloji a kokarin da ake yin a ganin an kara bunkasa harkokin ilimi a wannan kasa.
Wannan kokari da wannan burin a bunkasa ilimi da kaddamar da wannan kolojin ilimi ta yada addinin Musulunci abin jinjinawa ne matuka gaya kuma wani abu ne da ko shakka babu musulmin yankin za su cimma burin da amfanon da aka sa gaba.
697107