IQNA

Kimanin Musulmi Dubu Hamsin Ne Sun Sallaci Babbar Salla A Masko

Bangaren kasa da kasa; musulmi dubu hamsin ne suka taro a gaban masallacin cibiyar birnin Masko domin gudanar da shagulgulan babbar salla a ranar ashirin da biyar ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya nakalto daga majiyar labarai ta Interfax ya watsa rahoton cewa; musulmi dubu hamsin ne suka taro a gaban masallacin cibiyar birnin Masko domin gudanar da shagulgulan babbar salla a ranar ashirin da biyar ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.Musulmi na kasar Rasha da misalin karfe tara da rabi na safiya ne suka fara gudanar da taron shagulgulan tare da gudanar da sallar idi.

697129