IQNA

Baje Kolin Kur'ani Da Hadisai Da Jami'ar Almustapha (SWA) Ta Qum Ta Shirya

Bangaren al'adu da fasaha; a karo na biyu jami'ar Al'ustapha (SWA) Al'alamiya da ke birnin Qum da sauran cibiyoyi da ke karkashinta a dabra da kawo karshen gasar Kur'ani da hadisi na jami'ar da ake yi wa taken Olymapik na kasa da kasa na gasar Kur'ani da Hadisai sun shirya kasuwar baje kolin abubuwa da suka shafi kur'ani da Hadisai.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a karo na biyu jami'ar Al'ustapha (SWA) Al'alamiya da ke birnin Qum da sauran cibiyoyi da ke karkashinta a dabra da kawo karshen gasar Kur'ani da hadisi na jami'ar da ake yi wa taken Olymapik na kasa da kasa na gasar Kur'ani da Hadisai sun shirya kasuwar baje kolin abubuwa da suka shafi kur'ani da Hadisai.Mahdi Sabagi shugaban da ke kula da wannan kasuwar baje kolin a wata tattaunawa day a yi da kamfanin dillancin labarai na Ikna a birnin Qum ya bayyana cewa; wannan kasuwar baje kolin ta samun karbuwa da kuma ta shafi dakuna talatin inda mutane da dalibai ke ziyarta kuma sun nuna gamsuwa da kyayatarwa ta dukan bangarori.


697800