Bangaren kasa da kasa; a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa ne za a gudanar da taron yancin addini da lamarin da ya shafi kananan kabilu a yankin gabas ta tsakiya kuma a ranar daya ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya za a gudanar karkashin kulawar mu'assisar al'adun Musulunci da ke birnin Paris fadar mulkin kasar ta Faransa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa ne za a gudanar da taron yancin addini da lamarin da ya shafi kananan kabilu a yankin gabas ta tsakiya kuma a ranar daya ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya za a gudanar karkashin kulawar mu'assisar al'adun Musulunci da ke birnin Paris fadar mulkin kasar ta Faransa. A wannan taro za a samu halartar Saba mahmud lamanin sanin halayyar dan adam da al'adu a jami'ar Californiya na Amerika da kuma Jan Bubaro masanin tarihi da zamantakewar jama'a da addinai da kuma Anabul Barl da sauran manyan baki da malamai.
697795