IQNA

A Senegal An Watsa Littafin Tattaunawa Tsakanin Addinai Da Al'adu

Bangaren kasa da kasa; littafin tattauanwa tsakanin al'adu da kuma al'adu da Muhammad Habib Kebe lamamin ilimin sanin addinai da kuma mai bawa jami'ar San Luis shawara an watsa shi a kasar Senegal.





Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta aps ya watsa rahoton cewa; littafin tattauanwa tsakanin al'adu da kuma al'adu da Muhammad Habib Kebe lamamin ilimin sanin addinai da kuma mai bawa jami'ar San Luis shawara an watsa shi a kasar Senegal. Wannan littafi dai ya kumshi shafuka dari biyu da goma sha uku da kuma gurin bud=ga littafai na Silex- Nouvelles du Sud ta buga. Kuma akwai malamai da dama da suka sa hannu wajen rubutawa da dubawa kafin a buga shi kamar malamin jami'a Sheikh Hamidu Kane masanin ilimin zamantakewa da Musulunci a kasar ta Senegal inda ya rubuta wajibcin gudanar da tattaunawa a tsakanin al'ummomi daban daban da kuma ya ce wannan wani abu ne da tarihi ya tabbatar da hakan domin a sauran zamunan da suka gabata da kuma wanda ake ciki da sauran zamanoni masu zuwa ana bukatar yin hakan.

705513