Bangaren al'adu da fasaha:ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Tanzaniya sun aike da Fayfan Kamfiyota Na DVD da ya kumshi dubban littafai da majalloli a kasuwar baje kolin littafai na kasa da kasa a wannan kasa ta Tanzaniya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Tanzaniya sun aike da Fayfan Kamfiyota Na DVD da ya kumshi dubban littafai da majalloli a kasuwar baje kolin littafai na kasa da kasa a wannan kasa ta Tanzaniya.Wannan shi ne karo na sha tara a kasuwar baje kolin kasa da kasa ta littafai a Tanzaniya inda ofishin al'adu na jamhuriyar Musulunci ta Iran a Tanzaniya za ta halarta da kuma za a gudanar da shi a ranar hudu ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a otel din Ubungupalaza a birnin Darul Salam. A wajen wannan taron a ranar budewa za a samu halartat Walter Bi Guba Bamwita shugaban komitin yada littafai a kasar ta Tamzaniya.
707412