Bangaren siyasa da zamantakewa; a daidai lokacin kuratowar ranekun farko na watan Muharram da kuma na ashura na zagayowar shahadar Imam Huseini (AS) kungiyar gwagwarmaya Musulunci a Labanon Hizbullahi za ta fara gudanar da tarorrukan juyayi na shahadar Imam Huseini (AS).
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a daidai lokacin kuratowar ranekun farko na watan Muharram da kuma na ashura na zagayowar shahadar Imam Huseini (AS) kungiyar gwagwarmaya Musulunci a Labanon Hizbullahi za ta fara gudanar da tarorrukan juyayi na shahadar Imam Huseini (AS). Reshen kamfanin da ke kasar Labanon ne ya habarto cewa; dukan shagulgula sun kammala da kuma kafa haimomi na fara tarorrukan ashura a kauyuka da biranai na kuduncin kasar ta Labanon kuma daga misalin karfe uku da kwata na kowace rana agogon kasar za a fara a gaf da makarantar sakandri ta gwamnati a garin Sur yayin da a birnin Bint Jubail a babban dakin taro na Ahlul Baiti (AS) a a dandalin Albarka za a gudanar da misalin karfe shidda na kowace rana. Da sauran gurare da aka shirya da lokutansu cikin tsari.
707459