Bangaren kasa da kasa : a ranar ashirin da biyu ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin la Courneuve dake kewayen birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa aka fara gudanar da tarurrukan juyayin shahadar Shahidan Karbala a kungiyar Mahfalul Zainab (AS) ta shirya
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta mehfile Zainab ya watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da biyu ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin la Courneuve dake kewayen birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa aka fara gudanar da tarurrukan juyayin shahadar Shahidan Karbala a kungiyar Mahfalul Zainab (AS) ta shirya. A kowace rana da misalin karfe biyar saura kwata ne na agogon kasar ta Faransa za a fara gudanar da wannan taro tare da halartar yan shi'a da masu kaunar zuriyar gidan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa za su hallara kuma ana bude taron ne da karatun Alkur'ani mai girma sai kuma jawaban juyayi da tausayawa.
711823