Bangaren kasa da kasa: Bayan kawo karshe baje kolin kasa da kasa ta littafai a Bairut karo na hamsin da hudu ,cibiyar bincike ta hauzar ilimi ta birnin Qum Nur ta yi sa'ar halartar wannan kasuwar baje koli a karo na goma sha daya da kawo littatafai da aka buga cikin sabon salo irin na zamani.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Bayan kawo karshe baje kolin kasa da kasa ta littafai a Bairut karo na hamsin da hudu ,cibiyar bincike ta hauzar ilimi ta birnin Qum Nur ta yi sa'ar halartar wannan kasuwar baje koli a karo na goma sha daya da kawo littatafai da aka buga cikin sabon salo irin na zamani.Ali Rida Ahmadlo shugaban kasuwar baje kolin bangaren waje a cibiyar Nur a tatttaunawar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Ikna bayan ya yi bayani dalla-dalla kan wannan kasuwar baje kolin ya kara da cewa; a wajen wannan kasuwar baje kolin ta kasa da aksa an samu halartar mu'assishishi guda dari biyu daga kasashe kimanin ashirin na duniya.
714326