IQNA

A Riyad An Kafa Wata Cibiyar Mu'ijizar Ilimi A Kur'ani Da Sunnar Ma'aiki

Bangaren kasa da kasa: Jami'ar Musulunci ta Muhammad Bin Sa'ud dake birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiya an bude cibiyar nazarin muijizar ilimi da ke tattare a cikin kur'ani mai girma da kuma sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayansa.
Kamfanin dillancin labarai da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan nakaltowa daga majiyar labarai ta Muhit ya watsa rahoton cewa; Jami'ar Musulunci ta Muhammad Bin Sa'ud dake birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiya an bude cibiyar nazarin muijizar ilimi da ke tattare a cikin kur'ani mai girma da kuma sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayansa. Burin kafa wannan cibiyar shi ne bada dama ga duk wani bincike da nazari na ilimi da kuma sanin irin falalar ilimi da ke tattare a cikin ayoyin kur'ani da kuma hadisan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare da kuma alayan gidansa tsarkaka.


715801