Bangaren kasa da kasa;Said Muhammad Bakir Almij=hri wakilin maraji'I a kasar Koweiti a dalilin zagayowar ranar haifuwar Annabi Isa (AS_ a wannan shekara ta dubu da goma sha daya ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake taya dukan mabiya addinin kiristanci na duniya murnar zagayowar wannan rana ta farin ciki da murna da fatar Allah ya maimaita mana amin.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar jaridar ta kasar Koweiti Alkabas ya watsa rahoton cewa: Said Muhammad Bakir Almij=hri wakilin maraji'I a kasar Koweiti a dalilin zagayowar ranar haifuwar Annabi Isa (AS_ a wannan shekara ta dubu da goma sha daya ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake taya dukan mabiya addinin kiristanci na duniya murnar zagayowar wannan rana ta farin ciki da murna da fatar Allah ya maimaita mana amin. A cikin bayani ya yi bayani kan yadda Alkur'ani mai girma ya yi bayani da kawo labarin Annabi Isa (AS) da kuma musulmi da kiristoci ke farin ciki da zagayowar ranar Haifuwar wannan Bawon Allah da kuma yayi fatar wannan sabuwar shekara ta miladiya ta zamo shekara mai albarka da sa'ada ga al'ummar duniya musulmi da kiristocinsu.
717385