Bangaren kasa da kasa:Wasu daga cikin fitattun yan shi'a da sunna a kasar Saudiya a garin Madina Munarwara sun sanya hannu a wata yarjejjeniyar sulhu da fahimtar juna.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan nakaltowa daga majiyar labarai ta Rasid ya watsa rahoton cewa; Wasu daga cikin fitattun yan shi'a da sunna a kasar Saudiya a garin Madina Munarwara sun sanya hannu a wata yarjejjeniyar sulhu da fahimtar juna. A marecen ranar laraba hudu ga watan dai ne na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya sun sa hannu kan wata yarjejeniyar sulhu da fahimtar juma kuma wannan yarjejeniya za ta taimaka ko shakka babu wajan inganta zaman tare da fahimtar juna a tsakanin musulmi musamman a wannan kasa ta Saudiya.
718377