IQNA

Bukatar Karantar da Dokokin Shariar Musulunci A Makarantun Yan Waje A Dubai

Bangaren kasa da kasa; masana harkokin ilimi da koyarwa da kuma yada addinin Musulunci a birnin Dubai na Hadeddiyar Daular Larabawa sun bukaci wajabta koyar da dokokin shari'ar Musulunci da harshen larabci a makarantu musamman gay an kasashen waje da makarantunsu a Dubai.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin Kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta gulftimes ya watsa rahoton cewa: masana harkokin ilimi da koyarwa da kuma yada addinin Musulunci a birnin Dubai na Hadeddiyar Daular Larabawa sun bukaci wajabta koyar da dokokin shari'ar Musulunci da harshen larabci a makarantu musamman gay an kasashen waje da makarantunsu a Dubai. Masanan sun yi bayani kan dalilan yin hakan da kuma yadda koyar da harshen larabci zai taimakawa yan kasashen waje wajen fahimta da sanin shari'ar Musulunci da zamantakewar musulmi.


727094