IQNA

Gudanar Da Tarukan Tunawa Da Shahadar Sayyida Ruqayya (SA) A Afirka Ta Kudu

Bnagaren ilimi, An gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyida Ruqayya (SA) a kasar Afirka ta kudu, wanda ofishin bunkasa al’adu da ilimi na jamhuriyar musulunci ta Iran da ke kasar ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, tare da halartar malamai da kuma masana daga sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyida Ruqayya (SA) a kasar Afirka ta kudu, wanda ofishin bunkasa al’adu da ilimi na jamhuriyar musulunci ta Iran da ke kasar ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, tare da halartar malamai da kuma masana daga sassa daban-daban na kasar ta Afirka ta kudu.
An gudanar da wannan taro ne a bban ginin makarantar Imam Khomeni (RA) da ke birnin Pritoria fadar mulkin kasar Afirka ta kudu, haka nan kuma baya ga malamai da masana, daruruwan daliban wannan makaranta sun samu halartar taron, inda ak agabatar da jawabai kan matsayinta da kuma ayyukan da ta yi wa addinin muslunci.
Ggudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyida Ruqayya (SA) a kasar Afirka ta kudu, wanda ofishin bunkasa al’adu da ilimi na jamhuriyar musulunci ta Iran da ke kasar ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, tare da halartar malamai da kuma masana na kasar na nuni da ci gaban da aka samu ta fuskar addini.
729443