Bangaren al’adu da fasaha, An gudanar da zaman taro na karawa juna sani kan tarihin birnin Qods da kuma masallaci mai alfarma, da yadda yahudawan sahyuniya suka juya tarihin domin cimma manufofinsu na mamaya kan yankunan palalstinawa, tare da juya tarihin muslunci a yankin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labatri da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar Syria SANA an bayyan acewa, An gudanar da zaman taro na karawa juna sani kan tarihin birnin Qods da kuma masallaci mai alfarma, da yadda yahudawan sahyuniya suka juya tarihin domin cimma manufofinsu na mamaya kan yankunan palalstinawa, tare da juya tarihin muslunci a yankin na palastinu.
Rahoton ya kara da cewa a yayain gudanar dawannan zaman taro, masana tarihi daga kasashen musulmi, da kuam kasashen larabawa gami da wasu kasashen turai sun samu halarta, haka nan kuma da dam adaga cikinsu sun gabatar da jawabai kan tarihin birnin Qods da kuma masallaci mai alfarma, wanda ya tabbatar da makircin yahudawa na kokarin canja tarihin birnin damasallacin mai alfarma, wanda ke da matsayi na musamma gun musulmi.
Za a ci baga da gudanar da zaman taro na karawa juna sani kan tarihin birnin Qods da kuma masallaci mai alfarma, da yadda yahudawan sahyuniya suka juya tarihin domin cimma manufofinsu na mamaya kan yankunan palalstinawa, tare da juya tarihin muslunci a yankin a kowane wata.
729421