Bangaren al'adu da fasaha: a karon farko a birnin Rawilfandi na kasar Pakistan za a gudanar da olumpik na harshen farisanci da aka bawa taken zuwa ga gidan al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a karon farko a birnin Rawilfandi na kasar Pakistan za a gudanar da olumpik na harshen farisanci da aka bawa taken zuwa ga gidan al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran.Hukumar da ke kula da al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar sha biyu ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka gudanar da wannan da wannan olumpik na harshen farisanci inda yan jami'a da masana da dama suka halarci gurin.
742501